
Articles
-
Aug 27, 2023 |
hausa.premiumtimesng.com | Ashafa Murnai
-
Aug 27, 2023 |
hausa.premiumtimesng.com | Ashafa Murnai
Hukumomin Gwamnatin Tarayya biyu, CCB da EFCC sun fara binciken Shugaban Hukumar Ƙorafe-Ƙorafen Karɓar Rashawa da Cin Hanci na Jihar Kano, Muhyi Magaji. Kowace daga hukumomin biyu sun tura wa Hukumar KSPCAC ta Kano wasiƙar fara binciken shugaban ta Muhuyi Magaji. Kwanan baya ne dai Magaji ya bayyana cewa ya fara binciken zargin badaƙalar cushen dalolin da tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya yi a lokacin da ya na kan mulkin jihar Kano.
-
Aug 25, 2023 |
hausa.premiumtimesng.com | Ashafa Murnai
Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump, ya kai kan sa kurkuku, inda ya isa garin a cikin jirgin sa ƙirar Boeing 757. Magoya bayan sa na kiran jirgin da suna Trump Force One. Bayan saukar jirgin a filin jirgin Georgia, ya sauko ƙasa, ya sauko ƙasa, inda ya samu rakiyar jerin gwanon helikwaftoci waɗanda su ka yi tafiya a sama tsawon kilomita 22 zuwa Kurkukun Fulton. Ya isa kurkukun ƙarfe 7:30 na dare agogon EST. An yi masa rajistar dangwala yatsa, daga nan aka tsare shi.
-
Aug 25, 2023 |
hausa.premiumtimesng.com | Ashafa Murnai
An bayyana cewa a duniya kakaf, Najeriya ce ƙasa ta bakwai wajen yawan masu amfani da wayar hannu, wato wayar selula. Haka kuma ita ce ƙasa ta 11 a jerin masu yawan amfani da intanet a duniya. Mataimakin Shugaban Hukumar Sadarwa ta Ƙasa, Umar Ɗambatta ne ya bayyana haka, lokacin da ya ke magana wurin buɗe taron kwanaki biyu a kan bunƙasar kayan fasaha a hanyoyin sadarwa na tarho, ranar Alhamis, a Abuja. Ya ce Najeriya uwa ce sosai a harkokin sadarwar wayoyin tarho a Afirka.
-
Aug 25, 2023 |
hausa.premiumtimesng.com | Ashafa Murnai
Ministan Tsaro Mohammed Badaru, ya ce Najeriya za ta dangantaka da Birtaniya, domin samun nasarar daƙile matsalar tsaro. Badaru ya yi wannan bayani lokacin da ya ke karɓar baƙuncin Ministan Sojoji da Tsoffin Sojojin Birtaniya, James Heappey, a ofishin sa. Bayanin na cikin wata sanarwar da Daraktar Yaɗa Labarai ta Ma’aikatar Tsaro, Victoria Agba-Attah ta fitar. Baduru ya ce Birtaniya na bayar ga gagarimar gudummawar tabbatar da tsaro a ruwan Najeriya.
Try JournoFinder For Free
Search and contact over 1M+ journalist profiles, browse 100M+ articles, and unlock powerful PR tools.
Start Your 7-Day Free Trial →